Sudan Ta Kudu: Gwamnati Ta Tsagaita Wutar Yaki Ta Gefe Daya
Shugaban Kasar ta Sudan ta Kudu, Silva Kiir ne ya sanar da haka a yau litinin a wani yunkuri na farfado da tattaunawar sulhu.
Shugaban Kasar ta Sudan ta Kudu, Silva Kiir ne ya sanar da haka a yau litinin a wani yunkuri na farfado da tattaunawar sulhu.
Kamfanin dillancin labarun Anatoli na kasar Turkiya wanda ya nakalto shugaban na Sudan ta kudu yana jawabi, ya ci gaba da cewa; Wajibi ne kowa da kowa ya sani cewa tsagaita wuta ta fuskar abokan gaban ba wajibi ba ne, don haka sojojin gwamnati suna da hakkin kare kansu idan an kai musu hari.
Har ila yau Silva Kiir ya ce; An bai wa jami'an tsaron kasar, umarnin kada su kama duk wani dan hamayya wanda ya ke son shiga a tattauna da shi.
Tun a 2013 ne dai kasar ta Sudan ta kudu ta fada cikin yakin basasa a tsakanin sojojin da su ke biyayya ga shugaban kasa Silva Kiir da kuma tsaohon mataimakinsa, Reikh Machar.