Ivory Coast : An Kashe Mutane Uku A Yayin Wata Arangama
-
HOTO : Mashigar birnin Bouake (AFP)
Rahotanni daga Ivory Coast na cewa mutane uku ne suka mutu a yayin wata arangama tsakanin yan sanda da wasu tsaffin yan tawaye dake bukatar a basu kudade kamar sojojin da sukayi bore a makon jiya.
lamarin dai ya auku ne a yayin da tsaffin yan tawayen suka toshe hanyar shiga birnin Bouake dake tsakiyar kasar.
Kamfanin dilancin labaren AFP ya rawaito cewa na kai gawawakin mutane uku a babban asibitin birnin Bouake jim kadan bayan da yan sanda suka tarwatsa masu zanga zangar da suka toshe hanyoyin shiga birnin tun a jiya.
A kwanan baya ne gwamnatin Ivory Coast ta sanar da cimma matsaya da sojoji masu bore bayan fantsama kan tituna suna masu bore kan jinkirin da aka samu wajen biyansu kudaden alawas da gwamnati ta yi musu alkawari.