An Sauke Ministan Shara'a Na Kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20650-an_sauke_ministan_shara'a_na_kasar_sudan
An sauke Ministan shara'ar kasar Sudan daga kan mikaminsa kan laifin amfanin da takardun boge
(last modified 2018-08-22T11:30:09+00:00 )
May 23, 2017 18:06 UTC
  • An Sauke Ministan Shara'a Na Kasar Sudan

An sauke Ministan shara'ar kasar Sudan daga kan mikaminsa kan laifin amfanin da takardun boge

Kafar watsa labaran Alyaumu Sabi'i ta habarta cewa a wannan Talata Shugaban kasar Sudan Umar Albashir ya sauke Ministan shara'ar kasar Abubakar Hamad daga kan mikaminsa tare da mayar gurbinsa da Abas Muhamad Taha, Shi dai Abubakar Hamad ana zarkinsa ne da amfani da takardar digirin digirgir na boge.

Kafin a bashi wannan mikami na Ministan Shara'a Abubakar hamad ya gabatar da digirinsa wato digirin digirgir a fanin ilimin shara'a daga jami'ar Northwestern ta kasar Amurka.

Duk da cewa tsohon Ministan ya kasa gabatar da wani dalili da zai tabbatar da da'awarsa to saidai yayi watsi da zarkin da ake yi masa na amfanin da digirin boge.

Baya ga hakan Gwamnatin kasar Sudan din ta dakatar da tsohon Ministan daga duk wani aiki na Gwamnati saboda yayi amfani da digirin boge wanda ake gani a matsayin cin amanar kasa.