Morocco : An Dage Shari'ar Yan Jaridan Da Ake Tsareda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20702-morocco_an_dage_shari'ar_yan_jaridan_da_ake_tsareda
A kasar Morocco an dage sharia'a da akewa wasu yan jadira da masu fafatuka bakwai bisa zarginsu da kawo cikas ga tsaron kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
May 25, 2017 06:46 UTC
  • Morocco : An Dage Shari'ar Yan Jaridan Da Ake Tsareda

A kasar Morocco an dage sharia'a da akewa wasu yan jadira da masu fafatuka bakwai bisa zarginsu da kawo cikas ga tsaron kasar.

An dai dage zamen shariá mutanen ne har zuwa ranar 11 ga watan Oktoba na wannan shakara a cewar wata majiya kusa da masu zargin.

A jiya ne dai aka gurfanar da mutanen da suka hada da masanin tarihin nan Maati Monjib a kotun birnin Rabat.

Wannan dai shi ne karo na shida da ake dage shari'ar mutanen da aka fara a watan Nowamba na shekara 2015.