D.R Kongo : Karamcin Abinci Na Barazana Ga Yara 400,000
May 25, 2017 06:46 UTC
Asusun kula da yara kankanan yara na MDD wato Unicef ya yi kururuwar cewa yara kimanin 400,000 ke fuskantar barazanar matsananciyar yinwa a yankin Kasai na Jamhuriya Demukuradiyyar Kongo.
Matsalar na kara kamari ne a cewar Asusun na Unicef saboda rikicin dake ci gaba da faruwa a yankin.
A rahoton data fitar jiya Laraba Unicef ta nuna matukar damuwa akan yanayin da ake ciki a yankin a watannin baya bayan nan wanda ta ce tana bukatar kudade sama da Dala Milyan arba'ín cikin gaggawa domin tunkarar matsalar.
Tun kafin barkewar rikici a yankin dama Kasai na daya daga cikin yankunan dake fama da talauci a wannan kasa ta D.R Kongo.
Tags