Zambiya Ta Hana Jagoran 'Yan Adawan Afirka Ta Kudu Shiga Kasarta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20738-zambiya_ta_hana_jagoran_'yan_adawan_afirka_ta_kudu_shiga_kasarta
Hukumomi a Zambiya sun hana jagoran 'yan adawa na Afrika ta Kudu sanya kafa a kasar saboda goyan bayan madugun 'yan adawan kasar ta Zambiya da yake yi.
(last modified 2018-08-22T07:00:09+00:00 )
May 26, 2017 05:16 UTC
  • Zambiya Ta Hana Jagoran 'Yan Adawan Afirka Ta Kudu Shiga Kasarta

Hukumomi a Zambiya sun hana jagoran 'yan adawa na Afrika ta Kudu sanya kafa a kasar saboda goyan bayan madugun 'yan adawan kasar ta Zambiya da yake yi.

Jam'iyyar (DA) a Afrika ta Kudu ta ce an hana jagoran na ta Mmusi Maimane shiga Zambiya domin halartar zamen shari'a madugun adawan na Zambiya Hakainde Hichilema.

Bayanan da Jam'iyyar ta Demucratique Alliance ta fitar sun ce 'yan sanda Zambiya din sun shiga cikin jirgin da Mista Maimane na Afrika ta Kudun ke ciki suka kuma hana shi sauka daga cikin jirgin.

Shi dai takwaran nasa na Zambiya M. Hichilema, mai shekaru 54 ana tsare da shi ne tun farkon watan Afrilu bisa laifin cin amanar kasa, ta hanyar kawo cikas ga ayarin motocin shugaban kasar Edgar Lungu.