Guinea Bissau : 'Yan Sanda Sun Tarwatsa Zanga-zangar Masu Kyammar Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20780-guinea_bissau_'yan_sanda_sun_tarwatsa_zanga_zangar_masu_kyammar_gwamnati
Rahotanni daga Guinea Bissau na cewa 'yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar lumana ta neman shugaban kasar Jose Mario Vaz, da ya yi murabus.
(last modified 2018-08-22T07:00:10+00:00 )
May 27, 2017 11:15 UTC
  • Guinea Bissau : 'Yan Sanda Sun Tarwatsa Zanga-zangar Masu Kyammar Gwamnati

Rahotanni daga Guinea Bissau na cewa 'yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar lumana ta neman shugaban kasar Jose Mario Vaz, da ya yi murabus.

Kimanin masu zanga-zanga dubu biyu ne suka bisa kiran wasu kungiyoyin fara hula na kasar suka shiga jerin gwanon lumana na yau Asabar a Bisau babban birnin kasar.

Masu aiko da rahotannin sun ce masu zanga-zanga da suka nufi fadar shuigaban kasr sun yi ta kone-konen tayoyi, an kuma rawaito jinkatar yan sandu hudu.

Kungiyoyin dai na bukatar murabus din gwamnatin kasar saboda rikicin siyasar da yaki ci yaki cinyewa tsakanin jam'iyyar PAIGC da Mista Vaz.

Shugaban Mario Vaz ya yi firicin cewa zai gaba da mulkin kasar ta ko wanne hali domin cimma manufofinsa na ciyar da kasar a gaba.