Mukaddashin Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Shirin Samar Da Ruwa A Zaria
Mukaddashin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin bada ruwan sha a birnin Zaria na jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa a jawabin da ya gabatar a wajen kaddamar da shirin Osinbajo ya bayyana cewa jam'iyyar APC karkashin gwamna Nasir El-Rufaee ta kammala shirin samar da ruwa a birnin Zaria cikin shekaru 2 kacal a yayinsa gwamnatocin da suka gabata suka kasa kammala shi a shekaru 16.
John Oyegun, shugaban Jam'iyyar APC wanda ya wakilci mataimakin shugaban kasa a bikin bude aikin samar da ruwan sha na kimanin lita miliyon 150 a yayi jinjinawa gwamnan jihar ta Kaduna kan kammala wannan gagarumin aikin ya kuma bukaci mutanen zaria wadanda suka shafe shekaru kimani 40 suna fama da karancin ruwa zasu yi amfani da shi kamar yadda ya dace.
Amma wata majiya ta Jaridar Dail Trust ta nakalto shugaban mataimakin shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar ta Kaduna Alhaji Namadi Sambo yana cewa shene ya fara wannan aikin a shekara ta 2008 kuma tun lokacin da ya bar kujerar gwamna ba wanda ya kara wani abu kan abinda ya bari.