An Bude Talabijin Ta Muslunci A Malawi A Farkon Ramadan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20800-an_bude_talabijin_ta_muslunci_a_malawi_a_farkon_ramadan
An bude talabijin ta muslunci ta farko a kasar Malawi a daidai lokacin da ake fara azumin watan Ramadan mai alfarma.
(last modified 2018-08-22T07:00:10+00:00 )
May 28, 2017 06:42 UTC
  • An Bude Talabijin Ta Muslunci A Malawi A Farkon Ramadan

An bude talabijin ta muslunci ta farko a kasar Malawi a daidai lokacin da ake fara azumin watan Ramadan mai alfarma.

Shafin yada labarai WB cewa, an bude wannan tasha ne mai suna TV Islam, da nufin gudanar da shirye-shirye da suka danganci addinin muslunci da yada zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin musulmi da sauran addinai.

A lokutan baya musulmin kasar Malawi suna kallon tashoshin muslunci, amma ba nasu ne na cikin gida ba, saboda haka abubuwa da dama da suke bukatar sani da suka shafe su da yanayin zamantakewarsu na yi musu wahala matuka ta hanyoyin tashoshin talabijin, ganin su ne kashi 30 cikin kamutane miliyan 17 na kasar.

Jadun Montali shi ne ministan yada labarai na kasar ta Malawi, ya halarci taron kaddamar da wannan gidan talabijin a jiya, inda ya bayyana jin dadinsa matuka dangane da hakan, yana mai cewa hakika ya yi farin cikin bude wanan tasha, wadda za ta kara taimakawa wajen yada zaman lafiya da fahimtar juna a kasarsa.