Osinbajo Ya Bayyana Nasarorin Da Gwamnatinsu Ta Samu Cikin Shekaru Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20834-osinbajo_ya_bayyana_nasarorin_da_gwamnatinsu_ta_samu_cikin_shekaru_biyu
Yau Litinin ta kasance ranar dimokuradiyya a Najeriya, ranar da a bana ta zo daidai lokacin da shugaban da ke kan karagar mulkin kasar Muhammadu Buhari ya cika shekaru biyu da rantsuwar kama aiki.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
May 29, 2017 13:47 UTC
  • Osinbajo Ya Bayyana Nasarorin Da Gwamnatinsu Ta Samu Cikin Shekaru Biyu

Yau Litinin ta kasance ranar dimokuradiyya a Najeriya, ranar da a bana ta zo daidai lokacin da shugaban da ke kan karagar mulkin kasar Muhammadu Buhari ya cika shekaru biyu da rantsuwar kama aiki.

An gudanar da bikin na yau ne  a daidai lokacin da shugaba Buhari  ke jinya a kasar Birtaniya sakamakon rashin lafiyar da ya ke fama da ita, inda mukaddashinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya gabatar wa ‘yan kasar jawabi a madadinsa.

Jawabin mukaddashin shugaban kasar  ya mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa guda uku da suka hada da tsaro da yaki da rashawa da tattalin arziki.

Osinbajo ya ce ko shakka babu gwamnatinsu ta yi nasara sosai ta fannin tsaro musamman yakin da ake yi akan kungiyar Boko Haram, domin a yau ba wani yanki da ke karkashin ikon kungiyar, sannan gwamnatinsu ta yi nasarar ceto wasu daga cikin ‘yan Matan Chibok wadanda sace su ya tayar da hankalin duniya.Osinbajo ya bayyana cewa an samu nasarar samar da tsaro a yankin Neja Delta mai arzikin mai, kamar yadda aka samu irin wannan nasara a fagen yaki da rashawa sakamakon samun goyon bayan da al’umma ke bayarwa ne tsegunta wa hukumar yakin da cin hanci da rashawa

Mukaddashin shugaban kasar na Najeriya ya danganta matsalar tattalin arziki a matsayin babban kalubalen da gwamnatin Buhari ta fuskanta.inda“Tun lokacin da muka karbi mulki gwamnatinmu ta mayar da hankali ga matsalolin tattalin arzikin musamman ma tasirinsa ga wahalhalun da ‘yan Najeriya suke ciki.

Daga karshe ,Osinbajo ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu’o’I domin samun sauki dangane da rashin lafiyar da ya ke fama ita a halin yanzu.Sannan kuma ya yi kira ga samar da hadin kai a tsakanin ‘yan kasa.