An Zargi Gwamnatin Kenya Da Take Hakkokin 'Yan Jarida A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20908-an_zargi_gwamnatin_kenya_da_take_hakkokin_'yan_jarida_a_kasar
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun zargi gwamnatin kasar Kenya da take hakkokin 'yan jarida masu zaman kansu a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:11+00:00 )
Jun 01, 2017 02:28 UTC
  • An Zargi Gwamnatin Kenya Da Take Hakkokin 'Yan Jarida A Kasar

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun zargi gwamnatin kasar Kenya da take hakkokin 'yan jarida masu zaman kansu a kasar.

Jaridar Lomond ta kasar Faransa ta bayar da rahoton cewa, wakilan kungiyoyin kare hakkin bil adama da ke birnin Nairobi sun bayyana yanayin da 'yan jarida suke ciki a kasar Kenya da cewa yanayi mai hadari, sakamakon irin barazanar da ake yi wa rayukansu.

Rahoton ya ce gwamnatin kasar ta kara daukar tsauraran matakai a kan ayyukan da 'yan jarida masu zaman kansu suke gudanarwa a kasar ne a daidai lokacin da zabukan kasar ke karatowa.

Tun a ranar 28 ga watan mayu da ya gabata ne aka bude yakin neman zabe a fadin kasar, a ranar 8 ga watan Agusta mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban kasa, da na 'yan majalisar dokoki da kuma na gwamnoni a kasar ta Kenya.