Allura Cutar Kyanda Ta Kashe Yara 15 A Sudan Ta Kudu
Ma'aikatar lafiya a Sudan ta kudu ta sanar da cewa wata gurbataciyar allura cutar kyanda ta yi ajalin yara 15 a yankin kudu maso gabas na kasar mai fama da rikici.
Da yake bayyana a wani taron manema labarai ministan lafiya na kasar, Riek Gai Kok, ya ce binciken da akayi ya gano wasu cututuka da kuma guba a cikin alluran wanda hakan ya yi ajalin yaran.
Ko baya ga hakan binciken ya gano cewa jami'an lafiya basu bi ka'idodin aikin hukumar lafiya ta duniya ba inda sukayi wa yaran shaushawa da allura guda a cikin kwanaki hudu na kamfe shaushawar.
Binciken wanda wani kwamitin Sudan ta kudun kwarare kan sha'anin kiwan lafiya da taimakon kwararu na hukumar lafiya ta duniya WHO da Unicef ya gudanar ya kuma nuna cewa ba'a bi ka'idar adana sinadaran allurar ta kyanda ba wanda ke bukatar sanyi wanda hakan ya gurbata su.
A farkon watan daya gabata ne yaran suka fara mutuwa, a yayin da wasu 32 na daban suka wahala sosai da cututukan iri daban daban da suka hada da amai, zazzabi, gudawa.