Taron Kungiyar ECOWAS Karo Na 51 A Laberia
Mayan batutuwan da taron zai maida hankali akansu sun hada da zaben wanda zai maye gurbin shugabar Laberia Ellen Johnson Sirleaf wacce ke rikeda shugabancin karba-karba na kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS ko CEDEAO).
A ranar hudu ga watan Yuni na shekara 2016 data gabata ce a birnin Dakar na Senegal, Mme Sirleaf ta karbi ragamar shugabanacin kungiyar daga hannun shugaba Macky Sall, na Senegal.
Bayan wa'addin shugabancin kungiyar na shekara guda, a yayin wannan taron karo na 51 ne Mme Sirlieaf za ta mika ragamar shugabancin ga daya daga cikin takwarorinta da aka zaba.
Bayan batun zaben wanda zai shugabanci kungiyar ta ECOWAS, shugabanin kasashe mambobin kungiyar za su maida hankali kan batutuwan da suka hada bukatar kasar Morocco na zama mamba a kungiyar, da kuma na Tunisia na neman matsayin zama kasa 'yar sa ido a kungiyar ta ECOWAS.
Ko baya ga hakan da akwai duba wata yarjejeniyar ta tsakanin kasar Mauritaniya da kungiyar.
A daya bangare kuwa shugabannin zasuyi nazari kan rahotanni da taron ministocin kungiyar karo na 78 ya gabatar da kuma na taron kwamitocin shiga tsakani da na tsaro na kungiyar karo na 38.
Haka zalika kuma da akwai yarjejeniyoyi da dama da taron na Monorovia zai rattabawa hannu, daga cikinsu da akwai na babbar hanyar biranen Dakar-Abidjan, da kuma dora tubalin farko na babban shirin nan na kasashen yankin na samar da wutar lantarki wanda ya shafi kasashen Ivory Coast, Laberia da kuma Saliyo.
Ana sa ran kuma gabatar da wasu batutuwa guda biyu a yayin wannan taron na yau da suka hada da na annobar Ebola, da kuma na 'yan jam'iyun siyasa kasar Laberia dake takara a babban zaben kasar.
Daga cikin wadanda zasuyi jawabi a taron da akwai shugaban da aka zaba, da wakilin sakatare janar na MDD a kasashen yammacin Afrika dana Sahel Dr Mohamed Ibn Chambas da kuma shugaban kwamitin kungiyar tarayya Afrika Moussa Faki Mahamat.
Baya ga su kuma da akwai babbar wakiliyar kungiyar tarayya turai mai kula da harkokin waje Federica Mogherini, da kuma fira ministan Isra'ila Benyamin Netanyahou da zasu jawabi ga mahalarta taron.
Shugabar kungiyar mai barin gado, Mme Ellen Johnson Sirleaf, wacce ita ce macce shugabar kasa ta farko a Afrika ce zata yi jawabin bude taron.
Saidai taron na bana ya zo ma wasu kasashen Afrika da dama da mamaki saboda gayyatar firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda hakan ne ma yasa wasu shugabannin kasashen Afrika da basu da wata hulda da hahudawan mamaya na Isra'ila a sahun gaba sarkin Morroco Mohamad na shida fasa zuwa taron.
Ko baya ga hakan kasashen Afrika da dama sun ce zasu aike ne da wakilai na jeka na yika ne a taron kawai kasancewarsu mamba a kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO.