An Yi Taho Mu Gama Tsakanin Magoya Bayan Jammeh Da Dakarun ECOMIG
Rahotanni daga kasar Gambiya sun bayyana cewar alal akalla mutane 6 sun sami munanan raunuka sakamakon wani fito na fito da aka yi tsakanin magoya bayan tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh da dakarun kungiyar ECOWAS wato ECOMIG da aka shigo da su kasar tun bayan rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar.
Rahotanni dai sun ce rikicin ya barke ne bayan da dakarun ECOMIG din suka iso gidan tsohon shugaba Jammeh din a kauyensu na Kanilai inda magoya bayan nasa suka fito don nuna rashin amincewarsu da kasantuwar dakarun a kusa da gidan tsohon shugaban.
An ce dakarun na ECOMIG sun yi amfani da harsasai masu rai wajen tarwatsa masu zanga-zangar lamarin da yayi sanadiyyar raunana wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaba Jammeh wasu ma an ce suna cikin mawuyacin hali sakamakon raunukan da suka samu.
Gwamnati ko kuma dakaru na ECOMIG ba su ce komai dangane da wannan lamarin ba da kuma dalilin zuwan dakarun gidan tsohon shugaba Jammeh wanda dakarun suka taimaka wajen kawo karshen mulkinsa na sama da shekaru 20 bayan shan kayen da yayi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a bara bayan da ya ki amincewa ya sauka daga mulkin.