Kungiyar AU Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Yarjejeniyar Paris
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta shigo sahun nuna rashin amincewarta da matsayar da shugaban kasar Amurka ya dauka na ficewa daga yarjejeniyar rage dumamar yanayi na Paris inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga yarjejeniyar da kuma yin komai wajen ganin an yi aiki da ita.
Shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Guinea Alpha Conde ne ya bayyana hakan inda ya ce duk da cewa kasashen Afirka ba su taka wani rawa na azo a gani wajen lalata yanayin, to amma kuma su ne suka fi cutuwa daga matsala da illar dumamar yanayi din.
Don haka sai shugaba Conde ya bukaci da a sake tattaunawa batun rage dumamar yanayin a taron kasashen G20 da za’a yi a kasar Jamus a wata mai kamawa.
A ranar Alhamis din da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janye Amurkan daga cikin yarjejeniyar ta Paris da aka cimma ta a shekara ta 2015 bayan wani taro da shugabanni da wakilan kasashe kimanin 195 suka gudanar a birnin Paris babban birnin kasar Faransa dangane da yadda za a rage dumamar duniya. Shugabanni da 'yan siyasa da masana daga kasashe daban-daban na duniya na ci gaba da Allah wadai da wannan mataki da Donald Trump din ya dauka.