Wasu Daruruwan Jama'a Sun Gudanar Gangami A Mahaifar Tsohon Shugaban Gambia
Jun 05, 2017 06:34 UTC
Wasu daruruwan jama'a sun gudanar da gangami a kauyen Kanilai mahaifar tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jameh, da ke neman dakarun ECOWAS su fice daga kauyen nasu.
Majiyoyin ma'aikatar harkokin cikin gida akasar ta Gambia sun sanar da cewa, masu zanga-zangar suna dauke da makamai, kuma suna yin kira ne ga gwamnatin kasar kan ta karbi ragamar tsaro da kanta a kauyen, maimakon dakarun kasashen kungiyar ECOWAS.
Wannan lamari ya tislata ma'aikatar harkokin cikin gida akasar at Gambia kiran taron tsaro na gaggawa, domin daukar matakan da suka dace a kan wannan lamari.
Tags