Ana Sa Ran Shugaba Buhari Zai Koma Najeriya Ranar Asabar Mai Zuwa
Wasu majiyoyi daga fadar gwamnatin Najeriya sun bayyana cewa, ana saran shugaban kasar Muhammadu Buhari zai koma gida daga birnin London a ranar Asabar mai zuwa.
A ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata ne, shugaba Buhari ya tafi birnin London don duba lafiyarsa bayan ya mika ragamar mulkin kasar a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
Uwargidan shugaban da ta ziyarci mai gidanta a London Hajiya A’isha Buhari ta ce, shugaban na murmurewa cikin gaggawa kuma nan kusa zai dawo gida, uwargidan Shugaban kasar Tana magana ne a safiyar yau Talata bayan da ta dawo daga birnin London, inda ta kai masa ziyarar mako guda.
Ta ce shugaban ya "godewa 'yan kasar kan addu'o'in da suke yi masa da kuma goyon bayan da suke bai wa Mukaddashinsa Yemi Osinbajo".
Sai dai rashin lafiyar shugaban tana janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus ya fuskanci kula da lafiyarsa.kuma har yanzu dai 'yan kasar ba su san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.