AU Ta Goyi Bayan Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Yankin Sahel
(last modified Tue, 06 Jun 2017 11:47:09 GMT )
Jun 06, 2017 11:47 UTC
  •  AU Ta Goyi Bayan Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Yankin Sahel

Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta bukaci a kafa Rundunar tsaron hadin gwiwa na kasashen yankin Sahel domin yaki da ta'addanci

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto federica  Mogherini babbar Jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai jiya Litinin a birnin Bamako na kasar Mali na cewa kafa Rundunar hadin gwiwa na yankin Sahel zai kalubalanci ta'addancin masu da'awar Jihadi, da masu safarar mutane zuwa kasashen Turai

Rundunar za ta ƙunshi dakaru daga ƙasashen Mali da Mauritania da Chadi da Burkina Faso da kuma Nijar, don yaƙi da ƙungiyoyi masu da'awar jihadi, da harkokin fasa-ƙwauri da kuma baƙin haure, kuma ana sa ran rundunar da ta kumshi dakarun dubu biyar za ta fara aiki a watan Maris na wannan shekara da muke ciki

Sahel yanki ne na kungiyoyi masu tsattauran ra'ayin addinin Islama da dama, da wasu ke da alaka da kungiyar al-Qaeda.