Harin Bam Ya Hallaka Mutane Uku A Kenya
Jami'an 'yan sandar Kenya sun sanar da cewa Mutane uku sun rasu sakamakon tashin Bam a kusa da babbar hanya ta gabashin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Edward Muvambvury Shugaban 'yan sandar arewa maso gabashin kasar Kenya na cewa a ranar Talatar da ta gabata wani Bam da aka dasa a kusa da babbar hanya ya tashi da wata Mata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar 'yan kasar uku, kuma an bayyana cewa Motar na kan hanyar ta ne na zuwa garin Leybo.
Wannan dai shi ne sabon harin ta'addancin da aka kai kasar Kenya kafin watanni biyu da gudanar da zabe a kasar.kafin hakan dai a watan Mayun da ya gabata, jami'an 'yan sandar kasar sun gargadi Al'ummar kasar da su yi taka tsantsan dangane da karuwar hare-haren ta'addanci a kasar, wannan gargadi na zuwa ne bayan sanar da shigar mayakan 'yan ta'adda na Ashabab cikin kasar.
Tuni dai kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar AlQa'ida ta dauki nauyin kai harin.