INEC Ta Yi Wa Sabbin Jam'iyyun Siyasa 5 Rajista A Nijeriya
Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya, INEC, ta sanar da yin rajista wa wasu sabbin jam'iyyun siyasa su biyar a kasar don fafatawa a zabubbukan da za a gudanar nan gaba a kasar musamman ma dai na shekara ta 2019 mai zuwa.
Kakakin hukumar ta INEC, Adedeji Soyebi, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce hukumar ta amince ta yi rajista wa wasu jam'iyyun siyasa su biyar da suka gabatar da bukatarsu, wanda hakan ya sanya a halin yanzu akwai jam'iyyun siyasa 45 kenan a Nijeriyan.
Sanarwa ta kara da cewa sabbin jam'iyyun da aka yi musu rajistan dai su ne:
(1). Young Progressive Party (YPP).
(2). Advanced Peoples Democratic Alliance (APDA).
(3). New Generation Party of Nigeria (NGP).
(4). All Democratic Peoples Movement (ADPM).
(5). Action Democratic Party (ADP).
A shekaran jiya Talata ce shugaban hukumar zaben , Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewa bayan taron da manyan kwamishinonin hukumar za su gudanar a jiya Laraba a Kaduna za a sanar da sunayen sabbin jam'iyyun da aka yi musu rajistan bayan bukatar hakan da kimanin jam'iyyun siyasa 95 suka gabatar wa hukumar na suna so a yi musu rajistan.