Najeriya : Mutane 14 Suka Mutu A Harin Maiduguri
Hukumomi a Najeriya sun ce mutane 14 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 24 suka jikkata a harin da ake dangantawa dana kungiyar boko Haram a garin Maiduguri.
Bayanai daga jami'an yan sanda yankin sun ce mayakan sunyi amfani da mayan bindigogi da kuma boma bomai wajen kaddamar da harin na yammacin jiya Laraba.
Da yake tabbatarwa da manema labarai da lamarin kwamishinan yan sanda jihar Borno, Damian Chukwu ya ce an kashe fararen hula ne a jerin hare-haren kunar bakin wake uku.
Mafi muni shi ne wanda wani dan kunar bakin wake ya kai a unguwar Goni-Kachallari a daidai lokacin jama'a ke fitowa daga cikin wani masallacin unguwar inda mutane shida suka mutu.
A watan daya gabata wani faifan bidiyo ya nuna daya daga cikin kwamandodin da gwamnatin kasar tayi musaya dasu da 'yan matan nan na Chibok su 82 ya yi barazanar kai hare-hare a Maiduguri.
Hare haren da kungiyar boko haram ke kaiwa tun a shekara 2009 sunyi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 tare da cilastawa wasu milyan 2,6 barin gudajensu.