Al'Shabab Ta Kai Mummunan Hari Kan Dakarun Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21144-al'shabab_ta_kai_mummunan_hari_kan_dakarun_somaliya
Kungiyar Al'shabab ta a Somaliya ce ta kai wani mummunan hari a wani inda ta kashe wani adadin sojoji mai yawa a wasu sansanin soji biyu dake yankin Puntland a arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:13+00:00 )
Jun 08, 2017 11:19 UTC
  • Al'Shabab Ta Kai Mummunan Hari Kan Dakarun Somaliya

Kungiyar Al'shabab ta a Somaliya ce ta kai wani mummunan hari a wani inda ta kashe wani adadin sojoji mai yawa a wasu sansanin soji biyu dake yankin Puntland a arewacin kasar.

Wasu bayanai da kungiyar ta fitar sun nuna cewa an kashe sojoji sama da 60, sai dai har kawo yanzu babu tabas akan sahihancin wadannan bayyanan daga hukumomin kasar ta Somaliya.

Amman wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, da sanyin safiyar yau wasu mahara da muggan makamai sun farmawa sansanin soji Af-Urur, dake yankin Puntland a arewacin kasar.

Wasu majiyoyi na daban a yankin sun ce an gwabza fada sosai inda kuma aka samu hassar rayuka da dama daga ko wanne bangare, saidai akwai sabani a cikin bayyanan da dakarun kasar da kuma wadanda 'yan al'shabab din suka bayar kan fadan da kuma adadin wadanda suka mutu.

shi dai kakakin kungiyar ta Al'shabab Sheikh Abdiaziz Abu Musab ya bayyana a gidan radiyon kungiyar Andalus cewa sun kashe sojoji 61 tare da awan gaba da motocin soji 16.

Idan ana tune a watan Fabrairu da ya gabata kungiyar ta Al'shabab ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa kan sabon shugaban kasar Mohamed Abdullahi Mohamed.