Shugaban Kasar Somaliya Ya Gargadi Kungiyar Al'shabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21168-shugaban_kasar_somaliya_ya_gargadi_kungiyar_al'shabab
Shugaban Kasar Somaliya Ya ce Sojojin Kasar Za Su mayar da martanin da ya dace ga kungiyar Ashabab
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jun 09, 2017 11:18 UTC
  • Shugaban Kasar Somaliya Ya Gargadi Kungiyar Al'shabab

Shugaban Kasar Somaliya Ya ce Sojojin Kasar Za Su mayar da martanin da ya dace ga kungiyar Ashabab

Hukumar gidan telbijin da radio ta kasar Iran ta nakalto Muhamad Abdullahi Muhamad Shugaban kasar Somaliya yayin da yake ishara kan harin ta'addancin da kungiyar Ashabab ta kaiwa Sansanin Sojin Af Urur dake arewa maso gabashin kasar wanda yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama a jiya Alkhamis na cewa shakka babu wannan harin na rashin imani da aka kaiwa Sojojin kasar za a mayar da martanin da ya dace.

A Cewar Shugaban kasar na Somaliya, Mayakan na Ashabab sun yi awan gaba da wasu Sojojin kasar, kimanin shekaru 25 kenan da kasar Somaliyar ke fuskantar hare-haren kungiyar Ashabab.

Bayan mamaye wani bangare na tsakiya da kudancin kasar da kungiyar Ashabab ta yi, a shekarun baya bayan nan Sojojin kasar tare da hadin gwiwar Dakarun kungiyar kasashen Afirka sun samu nasarar kwato manyan gariruwan kasar, inda yazu kawai wasu kauyuka ne na kudancin kasar suke rike a kalkashin ikon su.