Tarayyar Afrika Ta Yi Allah Wadai Da Hare Haren Ta'addanci Na Tehran
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi Allah Wadai Da Hare Haren ta'addanci wanda kungiyan yan ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin aiwatar da su a wurare biyu a nan Tehran a ranar Laraba da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Musa Mohammad shugaban tarayyar ta Afrika yana fadar haka a yau Jumma'a a cikin wani bayanin da ya fitar.
Mohammad ya kara da cewa hare haren ta'addanci a Tehran ya kara nuna mana wata fuska ta ta'addanci a duniya, ya ce kungiyar tarayyar Afrika AU tana yin Allah wadai da ayyukan ta'addanci a ko ina aka aiwatar da su a duniya. Sannan ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin Iran da kuma mutanen kasar. Musa Mohammad har'ila yau ya mika ta'aziyyar kungiyar ta musamman ga dangin wadanda musibar ta shafa kai tsaye a Iran.
A ranar Laraba da ta gabata ce wasu yan ta'addanci guda 5 suka kai hare hare kan mutane da jami'an tsaro a cikin majalisar dokokin kasar Iran da kuma haramin Imam Khumaini (q) a kudancin Tehran inda mutane 17 suka rasa rayukansu.