Rikicin Arewacin D/Congo Ya Sake Lashe Rayukan Mutane Biyu
Kimanin 'yan tawaye biyu ne suka rasa rayukansu a wata musayar wuta tsakanin Dakarun kasar D/Congo da 'yan tawayen a Jihar Ituri dake arewa maso gabashin kasar
A wata sanarwa da Carlos Kalombo kakakin Dakarun kasar Congon ya fitar a wannan Assabar, ya ce Sojojin kasar sun samu nasarar hallaka 'yan tawayen FRPI biyu a wata musayar wuta tsakanin da 'yan tawayen bayan da suka kawo musu hari a sansanin Sojin Kelenzi na jihar Ituri dake arewa maso gabashin kasar, kuma Sojojin sun samu nasarar tilastawa 'yan tawayen ja da baya.
Kakakin ya kara da cewa 'yan tawayen sun tayar da Bam kusa da wata Makaranta dake kauyen na Kelenzi, saidai kuma ya karyata jita-jitan cewa Sojojin kasar sun kwashe Dukiyoyin Al'umma a yankin.
A kwanakin baya-bayan nan ,Kasar Jumhoriyar Demokaradiyar Congon dai ta fada cikin wani yanayi na rashin tabas, bayan aikin kwashe al'ummar gabashin kasar da aka yi tare kuma da kaddamar da yaki a kan 'yan tawayen kabilar Hutu a gabashin kasar.