An Bukaci A Taimakawa Gwamnatin Somaliya Wajen Yaki Da Kungiyar Ashabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21228-an_bukaci_a_taimakawa_gwamnatin_somaliya_wajen_yaki_da_kungiyar_ashabab
Shugaban yankin Puntland na arewa maso gabashin Somaliya ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa su taimakawa Gwamnatin kasar wajen yakin kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab.
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 11, 2017 07:45 UTC
  • An Bukaci A Taimakawa Gwamnatin Somaliya Wajen Yaki Da Kungiyar Ashabab

Shugaban yankin Puntland na arewa maso gabashin Somaliya ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa su taimakawa Gwamnatin kasar wajen yakin kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Abdu Waly Muhamad Ali Shugaban yankin Puntland ya bukcin kungiyoyin kasa da kasa da su hada kai da Gwamnatin Somaliya wajen kawo karshen kungiyar ta'addancin Ashabab wanda hakan shi zai kawo karshen kisan fararen hula a kasar.

Har ila yau Muhamad Ali ya yi alawadai da harin ta'addancin da kungiyar Ashabab ta kai sansanin Sojojin Af-Urur dake yankin Puntland da yayi sanadiyar mutuwar mutane 30 tare da jikkata wasu da dama na daban, sannan kuma ya bukaci da a zagulo wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Kimanin shekaru 25 da kasar Somaliya ke fama da hare-haren ta'addancin na Kungiyar Ashabab, a baya dai kungiyar ta Ashabab ta mamaye wasu manyan gariruwan kasar, amma a shekarun baya-bayan nan a kwace su, abinda ya yi saura ba su fice wasu kananen kauyuka ba dake kusancin kasar.