Morocco: Gagarumar Zanga-Zangar A saki 'Yan Adawa A Ribat
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21238-morocco_gagarumar_zanga_zangar_a_saki_'yan_adawa_a_ribat
An gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a yau a birnin Ribat na kasar Morocco, domin neman a saki mutanen da jami'an tsaro suke tsare da su, sakamakon jagorantar wani gangami a yankin Husaimah da ke arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 11, 2017 17:09 UTC
  • Morocco: Gagarumar Zanga-Zangar A saki 'Yan Adawa A Ribat

An gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a yau a birnin Ribat na kasar Morocco, domin neman a saki mutanen da jami'an tsaro suke tsare da su, sakamakon jagorantar wani gangami a yankin Husaimah da ke arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar a birnin Ribat sun cika babban titin sarki Muhamad na 6 dsa ke tsakiyar birnin Ribat, inda tsawon sahun masu zanga-zangar ya kilo mita guda.

Wannan zanga-zanga dai tana zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaro suke ci gaba da kame jagororin boren jama'a a yankin Husaimah da ke arewacin kasar ta Morocco.

A cikin 'yan watannin baya-bayan nan ne Nasir Zafzafi wani matashi da ya rasa aikinsa ya fara jagorantar zanga-zanga domin yin kira ga gwamnati da ta mayar da hankali wajen samar wa matasa ayyukan yi, inda jami'an tsaro suka yi awon gaba da shi.

Daruruwa daga cikin masu zanga-zangar ta yau Ribat da suka hada da lauyoyi da kuma 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula, suna dauke da hotunan Nasir zafzafi.