FAO Za Ta Taimaka Ma Iyalai Dubu 900 A Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21266-fao_za_ta_taimaka_ma_iyalai_dubu_900_a_sudan_ta_kudu
Hukumar abinci ta mjalaisar dnkin duniya FAO ta sanar da cewa, tana da wani shiri na taimaka ma iyalai akalla dubu 900 a Sudan ta kudu domin shawo kan matsalar abinci da ake fama da ita a kasar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jun 13, 2017 02:18 UTC
  • FAO Za Ta Taimaka Ma Iyalai Dubu 900 A Sudan Ta Kudu

Hukumar abinci ta mjalaisar dnkin duniya FAO ta sanar da cewa, tana da wani shiri na taimaka ma iyalai akalla dubu 900 a Sudan ta kudu domin shawo kan matsalar abinci da ake fama da ita a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, a jiya Jacqueline Were daya daga cikin manyan jami'an hukumar abinci ta duniya ya sanar da cewa, za su samar da wasu kayan abinci cikin gaggawa ga iyalan da suke cikin bukatar taimako ta fuskar abinci a Sudan ta kudu.

Ya kara da cewa, baya ga haka kuma, suna da shirin yin aiki tare da ma'aikatar gona ta kasar, domin taimaka mutane ta fuskar noma, domin a samar da abinci wanda zai taimaka wajen yaki da yunwa a kasar, wanda zai magance matsalolin iyala akalla dubu 466.

Tun a karshen watan Disamban 2013 ne dai Sudan ta kudu ta fada a cikin rikici, bayan da shugaban kasar Salva Kiir ya kori mataimakinsa Reick Machar, wanda shi kuma ya shelanta tawaye.