An Kame Wasu Jami'an Tsaro A Congo Sakamakon Karbar Rashawa
An kame jami'an tsaro 30 a jamhuriyar Dimukradiyyar Congo sakamakon karbar cin hanci da rashawa.
Tashar radiyon Aukabi ta kasar Congo ta bayar da rahoton cewa, an kame jami'an tsaron ne a garin Goma babban birnin lardin Kievo ta arewa, bayan samunsu da laifin karbar cin hanci da rashawa a wani wurin tsaro da ake binciken ababen hawa, inda sukan karbi kudade daga matafiya da kuma 'yan kasuwa masu safara.
Bayan cafke jami'an tsaron da suka hada da sojoji da kuma 'yan sanda, an gurfanar da su jiya agaban wata kotun soji da ke birnin na Goma, alkalin kotun ya tabbatar da cewa jami'an tsaron za su fuskanci hukunci da ya dace da su, domin ya zama darasi ga duk wani jami'in tsaro mai aikata irin wannan aiki a kasar.