Osinbajo: Kasafin Kudin Shekara Mai Zuwa Zai Kammala A Cikin Watan Oktoba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21288-osinbajo_kasafin_kudin_shekara_mai_zuwa_zai_kammala_a_cikin_watan_oktoba
Mukaddashin shugaban kasa a tarayyar Nigeria Prof Yemi Osinbajo ya bayyana cewa kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2018 zai kammala a cikin watan Oktoba na wannan shekara.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Jun 13, 2017 13:26 UTC
  • Osinbajo: Kasafin Kudin Shekara Mai Zuwa Zai Kammala A Cikin Watan Oktoba

Mukaddashin shugaban kasa a tarayyar Nigeria Prof Yemi Osinbajo ya bayyana cewa kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2018 zai kammala a cikin watan Oktoba na wannan shekara.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto shugaban yana fadar haka ne bayan ya sanya hannu a kan kasafin kudin wannan shekara a fadar shugaban kasa. 

Shugaban ya kara da cewa a halin yanzu ana shirya kasafin kudi na shekara mai zuwa a cikin fadar shugaban kasa, inda ministan kasasfin kudi, ministan mata, ministan wutan lantarki, da kuma na ayyuka da gidaje da wasu wadanda abin ya shafa suna aiki a kansa. 

Osinbajo ya ce kasasfin kudin wannan shekara zai tafi kamar yadda aka tsara kan manya manyan ayyuka wadanda suka hada da farfado da tattalin arzikin kasa.  ya ce daga wannan shekara ta 2017-2020 gwamnatin kasar zata bada fifiko kan karfafa tattalin arzikin masu rauni a kasar, aikin noma da samar da abinci, samar da isasshen wutan lantarki da kuma man fetur. Daga karshe shugaba ya ce an ware naira billion biyu a kan manya manyan ayyuka kadai.

Har'ila yau shugaban zai gana da shuwagabannin arewa kan barazanar korar yan kabilar ibo daga arewacin kasar