Kungiyar IGAD Ta Jaddada Bukatar Kawo Karshen Yaki A Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21290-kungiyar_igad_ta_jaddada_bukatar_kawo_karshen_yaki_a_sudan_ta_kudu
Kungiyar raya tattalin arziki da kuma ci gaban kasashen tsakiyar Afrika ta jaddada bukatar a kawo karshen yaki a kasar Sudan ta Kudu.
(last modified 2019-01-16T07:30:45+00:00 )
Jun 13, 2017 17:56 UTC
  • Kungiyar IGAD Ta Jaddada Bukatar Kawo Karshen Yaki A Sudan Ta Kudu

Kungiyar raya tattalin arziki da kuma ci gaban kasashen tsakiyar Afrika ta jaddada bukatar a kawo karshen yaki a kasar Sudan ta Kudu.

Kamfanin dillancin labaran Xi Huwa na kasar China ya nakalto Hailemariam Desalegn Priministan kasar Ethiopia kuma shugaba karba karba na kungiyar ta IGAD yana  fadar haka a jiya litinin a taron shuwagabannin kasashen kungiyar wanda aka gudanar a birnin Adis-ababa.

Desalegn ya kara da cewa ci gaba da yaki ba zai taba samr da sulhu da zaman lafiya ba, don haka dole ne bangarorin biyu su amice da yerjejeniyar zaman lafiya da suka rattabawa hannu a shekara ta 2015 a birnin Adis-Ababa.

Kasashe 8 wadanda suka hada da Njibuti, Eriteria, Ethiopia, Kenya, Somalia, Sudan, Sudan ta Kudu da kuma Uganda, suna membobin kungiyar ta IGAD. 

Kasar Sudan ta kudu dai ta fada cikin yakin basasa tun shekara ta 2013 kuma duk kokarin da kasashen yankin suka yi na dakatar da yakin bai sami nasara ba.