Kimanin Mutane 10 Sun Musu Sakamakon Sabon Rikicin Afirka Ta Tsakiya
'Yan sandan kasar Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun sanar da cewa alal akalla mutane 10 sun rasa rayukansu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin wasu kungiyoyi biyu masu dauke da makami a garin Bambari da ke gabashin kasar.
Wasu rahotanni dai sun ce rikicin ya barke ne tsakanin wasu kungiyoyi masu dauke da makami da ba sa ga maciji da juna a tsakaninsu lamarin da yayi sanadiyyar kashe mutane 10 da kuma raunata wasu na daban.
Duk kuwa da cewa wasu rahotannin kuma suna danganta rikicin ne ga wasu masu satar shanu da suka jima suna cin karensu ba babbaka a yankin inda a wannan karon rikicin ya barke da yayi sanadiyyar mutuwar wannan adadi na mutane da wasu ma suka ce sun kai mutane 12.
Rikicin na jiya dai shine irin sa na farko da ya faru a kasar da ya lankwame irin wannan adadi na mutane tun bayan da aka rantsar da Faustin-Archange Touadera a matsayin sabon shugaban kasar.