An Tsawaita Dokar Ta- Baki A Tunusiya
Fadar shugaban kasa a Tunusiya ta bada sanarwar tsawaita dokar ta baci da wattani uku a kasar.
Yau dai kusan shekara guda da rabi kenan da ayyana dokar ta baki a wannan kasar ta Tunusiya, bayan jerin hare haren ta'addacin da kasar ta fuskanta.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce bayan tuntubar shugaban gwamnati da kuma kakakin majalisar wakilan al'umma, shugaba Beji Caïd Essebsi, ya dauki matakin tsawaita dokar da watanni hudu, wacce kuma zata fara aiki daga gobe Alhamis 15 ga wata.
Dokar dai ta baiwa jami'an tsaron kasar cikaken iko tare da hana duk wasu taruruka dakan iya tada zaune tsaye.
Gwamnatin Tunusiya ta ce iya kokarinta wajen yaki da ta'addanci, amman tana mai ci gaba da kiran a kara sa ido, da kuma bincike na gano sansanonin yan ta'adda a kasar.