Mukaddashin Shugaban Nigeria Ya Gargadi Ibo Kan Batun Ballewa
Mukaddashin shugaban Najeriya Prof. Yemi Osinbajo ya gargadi shuwagabannin kabilar ibo dangane da barzanar ballewan da matasan yankinsu ke yi.
Jaridar Dailytrust ta Nigeria ta nakalto mukaddashin shugaban yana fadar haka a jiya Laraba a lokacin da yake ganawa da shuwagabannin kabilar ta ibo a fadar shugaban kasa a Abuja.
Mukaddashin Shugaban ya kara da cewa "bai kamata mu yi shiru a kan kalamai masu tada hankali na ballewa daga kasar wadanda matasan kabilar ibo suke yi da kuma maida martanin da matasan arewa suka yi ba. Dole ne mu nemi hanyar kusantar juna a tsakanimmu".
Mukaddashin Shugaban ya kara da cewa yana da niyyar yiwa kungiyar gwamnoni kan wannan batun nan gaba. Osinbajo ya bukaci shuwagabannin ibo su dauki nauyin da ya hau kansu na nunawa mutanensu a binda ya dashe a matsayinsu na shuwagabanninsu.
Manyan manyan bakin da suka halarci taron tare da Osinbajo na jiya sun hada da shuwagabannin majalisun dokokin kasar biyu da kuma gwamnonin jihohin ibo wadanda suka hada da Enugu, Ebonyi, Anambra da Abia. Har'ila yau mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu, tsohon shugaban majalisar rattawa Ken Namani, da kuma Senatocin yankin