An Yi Garkuwa Da Mutane A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21332-an_yi_garkuwa_da_mutane_a_somaliya
Jami'an tsaron Somaliya sun samu nasarar kawo karshen garkuwar da aka yi da fararen hula a wurin cin abinci dake Magadushu babban Birnin Kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T11:30:15+00:00 )
Jun 15, 2017 11:08 UTC
  • An Yi Garkuwa Da Mutane A Somaliya

Jami'an tsaron Somaliya sun samu nasarar kawo karshen garkuwar da aka yi da fararen hula a wurin cin abinci dake Magadushu babban Birnin Kasar Somaliya

Tashar Telbijin din Al-Alam dake watsa shirye-shiryen ta daga nan birnin Tehran ta nakalto Jami'an 'yan sandar Somaliya na cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da Mutane da dama  a wajen wani cin abinci dake birnin Magadushu.

Rahotanni daga Somaliyan, na cewa dakarun tsaron kasar sun kawo karshen wannan Garkuwa  saidai a yayin fafatawar tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindigar, fararen hula 18 ne suka rasa rayukansu,yayin da wasu sama da 30 suka ji raunuka. Lamarin dai ya samo asali ne lokacin da wani dan kunar bakin wake da kuma wani dauke da bindiga suka afkawa gidan abincin 'Posh Treats' a jiya Laraba.

Tuni dai Kungiyar Ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar AlQa'ida ta dauki alahakin kai harin.