Hukumar Zabe A Nigeria Ta Bawa Sabbin Jam'iyyun Siyasa 5 Shaidar Rijista
Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Nigeria ta bawa sabbin jam'iyyun siyasa shaidar rijista a jiya Jumma'a.
Jaridar Premiumtimes ta Nigeria ta nakalto shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC Mahmood Yakubu yana bayya haka a jiya jumma'a a lokacinda yake mika takardun shaidar rijistan ga wadan nan jam'iyyun siyasa a Abuja.
Sabbin Jam'iyyun dai sun hada da Action Democratic Party (ADP), All Democratic People’s Movement (ADPM), Advanced People’s Democratic Alliance (APDA), New Generation Party of Nigeria (NGP) da kuma Young Progressive Party (YPP).
Shugaba hukumar zaben ya bukaci sabbin jam'iyyun da su dauki cewa samun rijista da suka yi a matsayin dama ce ta gudanar da harkokin siyasa a duk fadin kasar bisa dokokin zaben kasar da kuma sharuddan hukumarta.
Yakub ya kara da cewa hukumarsa zata ci gaba da sanya ido a kan ayyukan dukkan jam'iyyu siyada a kasar, kuma tana iya kwace rijistan ko wace jam'iyyaun siyasa wacce ta aikataka lamuran da suka cancanci hakan.