'Yan sanda Sun Kara Da Masu Zanga-Zanga A Kasar Morocco
(last modified Sat, 17 Jun 2017 19:16:42 GMT )
Jun 17, 2017 19:16 UTC
  • 'Yan sanda Sun Kara Da Masu Zanga-Zanga A Kasar Morocco

Zanga-Zangar da mutanen arewacin kasar Morocco suke yi tun ranar Alhamis da ta gabata ya sanya yan sandan kasar suka yi kokarin dakatar da ita da karfi, wanda ya kai sa insa da masu zanga-zangar.

Kamfanin dillancin labaran "News24" ya bayyana cewa yansanda a birnin Al-Husaimah daga arewacin kasar Morocco sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zangz-zanar da suka taru a wani wuri a birnin Al-Husaimah inda suke bukatar gwamnati ta saki Nasar Zafzafi shugaban yan adawan da suka kama a makon da ya gabata, ta kuma kyautata rayuwar mutanen yankin arewacin kasar.

Majiyar labarai daga yankin sun bayyana cewa wannan itace zanga-zangar ma fi muni a kasar Morocco tun shekara ta 2011. Zanga-zanga na baya bayan nan ta taso ne bayan kisan da yansanda suka yiwa wani mai saida kifi, suka kuma kwace kifin da yake sayarwa.

A halin yanzu dai yansanda sun gurfanar da Nasseer Zafzafi da wasu mutane 6 a gaban wata kotu a kasar inda suke zarginsi ta laifuffuka kimani 10.