CRA : An Cimma Yarjejeniyar Sulhu Tsakanin Gwamnati Da 'Yan Tawaye
Gwamnatin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ta ce ta cimma yarjejeniyar sulhu tsakaninta da ‘yan tawayen kasar a wani taron da aka yi a birnin Rome da niyar kawo karshen rikici a kasar.
Yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma a shiga tsakanin kungiyoyin addinin Katolika na Sant'Egidio ta tanadi tsagaita buda wuta na nan take da nufin samun zamen lafiya mai daurewa a duk fadin kasar.
Haka zalika yarjejeniyar ta kuma tanadi baiwa kungiyoyin dake dauke da makamai gurabe a gwamnati.
A bangaren tsaro kuma bangarorin sun dau alwashin samar da hanyoyin ingantatun safara jama'a da dukiyoyinsu ta hanyar bude shingayen da basu bisa ka'ida.
Kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, dai na fama da tashe-tashen hankula musamman na addini tun shekara ta 2013.