Rasha Ta Meka Jiragen Yaki Ga Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21518-rasha_ta_meka_jiragen_yaki_ga_kasar_masar
Rasha ta sanar da mekawa kasar Masar wasu Jiragen Yaki Samfarin K-52
(last modified 2018-08-22T11:30:16+00:00 )
Jun 20, 2017 18:07 UTC
  • Rasha Ta Meka Jiragen Yaki Ga Kasar Masar

Rasha ta sanar da mekawa kasar Masar wasu Jiragen Yaki Samfarin K-52

Kamfanin dillancin Labaran Rambler na kasar Rasha ya nakalto majiyar tsaron kasar na cewa bisa yerjejjeniyar sayan makamai tsakanin kasashen Rasha da Masar, kasar ta meka wasu jiragen yaki samfarin K-52 ga magabatan kasar ta Masar, rahoton ya ce wakilan Dakarun saman Masar ne suka karbi jiragen a cibiyar tsaro ta garin Arsenyev dake kusu maso gabashin kasar ta Rasha.

Har ila yau rahoton ya ce a halin yanzu akwai wani gungun Soja na mtukan jiragen yaki na Masar dake karbar horo na musaman a cibiyar tsaron garin  na Arsenyev.

A shekarar 2015 ne Kamfanin kirar Jiragen yakin Rasha ya kula yarjejjeniyar sayarwa Masar jirgen yaki samfarin K-52 guda 46 kuma shirin meka jiragen zai kamala kafin karshen wannan shekara ta 2017 da muke ciki.