Najeriya: Jami'an Tsaro Sun Kafa Dokar Hana Fita A Jahar Taraba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21532-najeriya_jami'an_tsaro_sun_kafa_dokar_hana_fita_a_jahar_taraba
Sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin 'yan kabilar Mabila da kuma Fulani a jahar Taraba, jami'an tsaro sun sanar da kafa dokar hana fita.
(last modified 2018-08-22T07:00:17+00:00 )
Jun 21, 2017 01:20 UTC
  • Najeriya: Jami'an Tsaro Sun Kafa Dokar Hana Fita A Jahar Taraba

Sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin 'yan kabilar Mabila da kuma Fulani a jahar Taraba, jami'an tsaro sun sanar da kafa dokar hana fita.

Majiyoyin tsaron sun tabbatar da cewa an dauki wannan matakin ne da nufin ganin an dakile yaduwar rikicin, da kuma tabbatar da doka da oda a fadin jahar.

Rikicin wanda ya barke kasa da mako guda da ya gabata, yana da nasaba ne da yunkurin da 'yan kabilar Mabila suka yi na karbar wasu filayen noma daga Fulani, amma kotu ta yanke hukuncin cewa fulani ne suke mallakar filayen, lamarin da ya fusata wasu daga cikin 'yan kabilar ta Mabila matuka.

Hukumomin tsaro sun ce mutum biyar ne suke da tabbacin sun rasa rayukansu, amma wasu majiyoyin na cewa adadin mutanen ad suka rasu sakamakon rikicin ya haura haka.