G5 Sahel : Kwamitin Tsaro Ya Amunce Da Kafa Rindinar Yaki Da Ta'addanci
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amunce da gagariminn rinjaye da bukatar kafa wata rindinar hadin gwiwa ta Afrika don yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi a yankin Sahel.
Kudirin wanda kasar Faransa ta gabatar da shi ya samu amuncewa daga mambobi 15 na kwamitin tsaron, bayan da mahukuntan Paris dana Washington suka cimma yarjejeniyar kan batutuwan da kudirin ya kunsa.
Kwamitin ya yi na'am da kudirin na jibge dakaraun kasashen na G5 Sahel da suka hada da (Mali, Mauritania, Nijar, Chadi da kuma Burkina Faso) saidai ba tare bada amuncewar MDD ba ga tawagar.
A watan Maris da ya gabata ne kasashen na Afrika biyar suka amunce da kafa rindinar ta hadin gwiwa da za ta kunshi dakaru 5,000 domin yaki da ta'addanci da safara miyagun kwayoyi da mutane a yankin na Sahel.
Tunda farko dai Amurka ta ki amuncewa da bukatar bisa cewarta babu cikaken bayyani a cikin kudirin, don haka ba'a bukatar gabatar da kudirin gaban mambobin kwamitin, kai tsaye ma zai iya amuncewa, saidai faransa ta ce ana bukatar amuncewar kasashe mambobin kwamitin kamar yadda kungiyar tarraya Afrika ta bukata.