MTN Ya Taimaka Wa Boko Haram A Najeriya, inji Shugaba Buhari
-
Shugaba Zuma da Buhari a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayana cewa kamfanin sadarwa na MTN mallakin kasar Afrika ta kudu ya taimaka wa ayyukan kungiyar Boko Haram, musamen kan rashin toshe miliyoyan layukan da ba a yi wa rijista ba.
Hukumomin Najeriya sun ci tarar MTN kusan dala biliyan 4 saboda laifin karya ka’ida wajen sayar da layukan da ba su da rajista.
A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai yau Talata kafin ya gana da Shugaban Jacob Zuma na Afirka ta Kudu dake ziyara a kasar, shugaba Buhari yace matsalar tsaro ce damuwar Najeriya.
Tun a tsakiyar 2015 hukumomi suka bukaci kamfanonin Sadarwa a Najeriya su toshe layukan da ba su da rijista, amma Kamfanin MTN ya ki bin ka’idar da hukumar sadarwa ta shata karkashin sabon tsarin yi wa mutane rijista saboda matsalar tsaro.
Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa mai yiwa ne bangarorin biyu suyi amfani da da ganawar su ta yau kan yadda za a warware batun kamfanin na MTN.