Najeriya : Mutane 15 Suka Mutu A Ruftawar Wani Bene A Lagos
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2161-najeriya_mutane_15_suka_mutu_a_ruftawar_wani_bene_a_lagos
Rahotanni daga Najeriya na cea mutane 15 ne suka rasa rayukan su sakamakon ruftawar wani bene mai hawa biyar da ake cikin ginawa a unguwar Lekki dake jihar Lagos.
(last modified 2018-08-22T06:57:57+00:00 )
Mar 08, 2016 14:04 UTC
  • wani gini daya ruta a Lagos (hoto rumbun ajiya)
    wani gini daya ruta a Lagos (hoto rumbun ajiya)

Rahotanni daga Najeriya na cea mutane 15 ne suka rasa rayukan su sakamakon ruftawar wani bene mai hawa biyar da ake cikin ginawa a unguwar Lekki dake jihar Lagos.

Bayanai sun nuna cewa daga cikin wandanda lamarin ya rusa dasu harda wata mata da jinjirin ta, sanan kuma akwai wasu 11 na daban da suka raunana kamar yadda Mal. Ibarhim Farinloye na hukumar agajin gaggawa ta NEMA ya tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP.

kawo yanzu babu cikaken bayani dangane da musababin ruftawar ginin, saidai tuni wasu suka fara danganta lamarin da rashin biyar ka'idodin gini.

wannan dai ba shi ne karon farko ba da irin hakan take faruwa a wannan jiha, inda ko a watan Satumba shekara 2014, mutane 116 galibi 'yan Afrika ta Kudu suka rasa rayukan su sakamakon ruftawar wani gini inda masu wa'azin kristoci na (TB Joshua) a arewacin Lagos suke da zama.