Barazanar Cutar Amai Da Gudawa Ga Yara A Yankin Tafkin Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21610-barazanar_cutar_amai_da_gudawa_ga_yara_a_yankin_tafkin_chadi
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya yi gargadin cewa, a lokacin da aka shiga yanayi na damina, sama da yara miliyan 5.6 ne ke cikin hadarin kamuwa da cututtukan da ake dauka daga ruwa a yankin tafkin Chadi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 24, 2017 09:56 UTC
  • Barazanar Cutar Amai Da Gudawa Ga Yara A Yankin Tafkin Chadi

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya yi gargadin cewa, a lokacin da aka shiga yanayi na damina, sama da yara miliyan 5.6 ne ke cikin hadarin kamuwa da cututtukan da ake dauka daga ruwa a yankin tafkin Chadi.

Daraktan shirin bada agajin gaggawa na Asusun Manuel Fontaine, ya bayyana cewa, barazanar barkewar cututtukan kamar kamar amai da gudawa a kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya, na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara fuskantar rashin tsaro, musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Asusun na Unicef ya kara da cewa ambaliyar ruwa da rashin kyawon hanyoyi, zai yi gagarumin tasiri wajen rage isar kayayyakin jin kai zuwa wurare masu nisa.

Manuel Fontaine ya kara da cewa, UNICEF da sauran hukumomin abokan huldarsa, na aiki a yankin na tafkin Chadi, a wuraren da ke fuskantar hadarin barkewar cutar amai da gudawa, inda suke ilmantar da iyalai illolin dake tattare da cutar da kuma matakan da za su iya bi na kare kawunansu.

Duk da rashin kudi, jami'in ya ce UNICEF a bana, ya kuduri aniyyar samarwa mutane miliyan 2.7 da tsaftataccen ruwan da suke bukata don rayuwa.