Gambia Tana Shirin Komawa Kungiyar Kasashe Renon Ingila Da Kotun ICC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21614-gambia_tana_shirin_komawa_kungiyar_kasashe_renon_ingila_da_kotun_icc
Kasar Gambia ta ce nan ba da dadewa ba za ta sake zama mamba a kungiyar kasashe renon Ingila da na kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa cewa da ICC.
(last modified 2018-08-22T07:00:17+00:00 )
Jun 24, 2017 10:29 UTC
  • Gambia Tana Shirin Komawa Kungiyar Kasashe Renon Ingila Da Kotun ICC

Kasar Gambia ta ce nan ba da dadewa ba za ta sake zama mamba a kungiyar kasashe renon Ingila da na kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa cewa da ICC.

Darektar watsa labarai da hulda da jama'a ta fadar shugaban kasar Amie Bojang-Sissoho wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce yanzu haka mahukuntar kasar na tattaunawa da sakatariyar kungiyar ta Commonwealth dake birnin London game da wannan batu.

A shekara ta 2013 ne dai tsohon shugaba Yahya Jammeh ya ayyana ficewar kasar ta Gambia daga kungiyar, yana mai ikirarin cewa, ba za a sake yiwa kasarsa wani mulkin mallaka ba.

Haka kuma a shekarar 2016 tsohuwar gwamnatin Jammeh ta sanarwa MDD shirinta na ficewa daga kasashe mambobin kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya, aman sabon shugaban kasar Adama Barrow ya takawa wannan shiri birki.