An Gano Wasu Kofai Masu Alaka Da Musulunci A Addis Ababa
Wasu masu gudanar da bincike a kan wuraren tarihi sun gano wani gari a kusa da birnin Addis Ababa na kasar Habasha da ke da alaka da musulmi.
Jaridar Independent ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, masu gudanar da binciken sun ce wurin yana dauke da wasu abubuwa na tarihi wadanda suke da alakada da kasashen musulmi kuma tarihinsu yana komawa zuwa ga shekaru fiye da dari bakawai a wani gari da kasa ta rufe shi kuma aka sake tono shi.
Daga cikin abubuwan da aka samu akwai tsoffin kayan karau da kuma duwatsun marmar da gilassai wadanda musulmi suke yin amfani da su daga kasashen Madagaska da Maldiv Yemen da kuma China.
Timosy Insel daga kasar Birtaniya masani ne a kan gano abubuwan tarihi ya bayyana cewa, akwai wani wurin kasuwanci da kuma masallatai da wasu cibiyoyi da aka samu a wurin, sun yi kama da ginin masallatan Tazania da kuma Somalia.
Ya ce ganin wadannan abubuwa ya sanya sun kara samun tabbaci a kan cewa wurin yana da alaka da musulmi, baya ga haka kuma sun samu kudade na zinari da azufa ga kuma tagwalla, wadanda aka yi musu zane da ke nuna alama ta musulunci.
Yanzu haka dai an dukufa wajen gudanar da bicnike a kan wadannan abubuwa domin kara samun tabbacia kansu da kuma tarhinsu.