Wakilin MDD Na Ziyarar Tuntuba a Burundi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21724-wakilin_mdd_na_ziyarar_tuntuba_a_burundi
Sabon wakilin musammen na MDD a Burundi, Michel Kafando ya isa birnin Bujumbura inda ake sa ran zai gana da mahukuntan kasar domin tuntuba.
(last modified 2018-08-22T07:00:18+00:00 )
Jun 28, 2017 07:50 UTC
  • Wakilin MDD Na Ziyarar Tuntuba a Burundi

Sabon wakilin musammen na MDD a Burundi, Michel Kafando ya isa birnin Bujumbura inda ake sa ran zai gana da mahukuntan kasar domin tuntuba.

Majiyoyin diflomatsiya sun ce Mista Kafando zai gana da ministan harkokin wajen kasar ta Burundi Alain-Aimé Nyamitwe, yau Laraba kafin daga bisani ya gana da shugaban kasar Pierre Nkurunziza a gobe Alhamis.

A ziyarar wacce it ace ta farko a matsayin ta tuntuba, ana sa ran kuma Kafando zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki kan rikicin siyasar kasar ta Burundi.

Ziyarar Jami’in an zuwa a cikin wani yanayi da dangantaka ta tabarbare tsakanin MDD da kuma mahukuntan Bujumbura.