Kasashe Da Dama Sun Hana Shigo Da Kaji Daga Afrika Ta Kudu
Jun 28, 2017 07:56 UTC
Kasashe makoftan Afrika ta kudu sun haramta shigo da kaji daga kasar bayan bullar wata mura tsuntsaye mai saurin yaduwa a Afrita ta kudun.
Kasar Namibia ta sanar da hana da shigo da kaji wanda ba dafaffu ba daga Afrika ta Kudun bayan sanar da bullar murar nau’in H5N8.
Dama kafin hakan kasashen da suka hada da Boswana, Zimbabwe, Mozambique da Zambia su ma sun dau irin wannan matakin saboda kaucewa haduwar murar.
A halin da ake ciki dai mahukuntan Afrika ta Kudu sun dau matakin hana sayar da kaji masu rai a duk fadin kasar.
Kwararu daga Afrika ta Kudu dai sun ce murar ta yadu ne ta hanyar wasu tsintsaye da suka shigo kasar daga Turai.
Tags