Tsohon Gwamnan Jihar Taraba A Nigeria Ya Mutu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21746-tsohon_gwamnan_jihar_taraba_a_nigeria_ya_mutu
Tsohon gwamnan jihar Taraba a arewa maso gabcin Nigeria Danbaba Sunrai ya rasu a wani asbiti a Amurka a jiya Laraba
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Jun 29, 2017 01:49 UTC
  • Tsohon Gwamnan Jihar Taraba A Nigeria Ya Mutu

Tsohon gwamnan jihar Taraba a arewa maso gabcin Nigeria Danbaba Sunrai ya rasu a wani asbiti a Amurka a jiya Laraba

Jaridar Daily trus ta Nigeria ta bayyana cewa tsohon gwamnan wanda ya yi hatsari da jirgin da yake tukawa dakansa a cikin watan Octoban shekara ta 2012 ya mutu a wani asbiti a birnin Houston na jihar Florida a kasar Amurka a jiya Laraba.

Mr Emmanuel Bello babban mai bawa gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku shawara kan al-amuran hulda da jama'a ya tabbatar wannan labari wa kamfanin dillancin labarai na Nigeria NAN.

Sutai dan shekara 56 a duniya  yana jinya tun bayan hatsarin na watan Octoba, a asbitoci daban daban a ciki da wajen kasar, kuma a halin yanzu ana shirye shiryen dawo da gawarsa zuwa gida nan kusa.