UNICEF Na Bukatar Dala Miliyan 22 Don Agazawa Yara A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21756-unicef_na_bukatar_dala_miliyan_22_don_agazawa_yara_a_sudan
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya yi shelar neman dala miliyan 22 cikin gaggawa, domin kai agajin jin kai ga yara sama da 100,000 a kasar Sudan.
(last modified 2018-08-22T07:00:19+00:00 )
Jun 29, 2017 05:21 UTC
  • UNICEF Na Bukatar Dala Miliyan 22 Don Agazawa Yara A Sudan

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya yi shelar neman dala miliyan 22 cikin gaggawa, domin kai agajin jin kai ga yara sama da 100,000 a kasar Sudan.

Yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba, wakilin UNICEF a Sudan Abdullahi Fadil, ya ce karuwar kwararar 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu da sama da mutane miliyan 2.3 da suka gujewa muhallansu a cikin kasar, na karawa al'ummomin da ke karbarsu nauyi.

Ya kara da cewa, yara ne ke ci gaba da fadawa haddura, kuma samun taimako mai dorewa na da mutukar muhimmanci wajen kai musu dauki a kan lokaci da samar da kayayyakin jin kai musamman ruwa da kayayyakin tsaftace muhalli da na kiwon lafiya da kuma sinadaran gina jiki.